エピソード

  • Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya A Najeriya
    2024/11/20

    An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya.

    A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai
    Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata.
    Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin, amma ga alama haƙa ta kasa cimma ruwa.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye harkar.

    続きを読む 一部表示
    25 分
  • Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci
    2024/11/13

    A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci.

    Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri bay a bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki.

    続きを読む 一部表示
    30 分
  • Tarihin Almajirci A Kasar Hausa Da Yadda Yake A Da.
    2024/11/06

    Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren larabci wato almuhajir, dake nufin wanda ya bar garin sa don zuwa wani gari neman ilimi.

    Mafi yawan alummar arewa inda akafi sanin Kalmar sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da musulunci ya fara shigowa Najeriya daga garin Maidugurin Jihar Borno zuwa kasar Hausa.

    Shirin Daga Larab na wannan mako yayi duba ne kan tarihin almajirci da kuma yadda yake a da can baya.

    続きを読む 一部表示
    24 分
  • Matsayin Gwamnonin Arewa Kan Kudurin Haraji – Kishin Kasa Ko Son Zuciya?
    2024/10/30

    Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuria’a.
    Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa.

    Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya?

    Wannan ce muhawarar da ta biyo bayan sanarwar bayan taron na NGF, kuma shirin Daga Laraba zai lalubo amsarta.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Shin Duka Ne Hanyar Ladabtar Da Yara Mafi Inganci?
    2024/10/23

    Tarbiyya kamar yadda aka san ta a al’adance tana inganta ne idan al’umma gaba daya ta hada hannu wajen ladabtar da yara.

    Duk wanda ya kai shekaru talatin zuwa sama ya san cewa a da can iyaye da sauran jama’ar gari suna iya daukar tsumagiya don ladabtar da shi idan ya kauce hanya.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne kan alfanun ko illar hakan wajen ladabtar da yara.

    続きを読む 一部表示
    26 分
  • Me Ya Sa Kimar Dattawa Ta Ragu A Cikin Al’umma?
    2024/10/16

    Afrika na da dadadden tarihin girmama na gaba, musamman dattawan da ke cikin al’umma.

    Sai dai a wannan zamani akan samu matashi ya shafa wa idonsa toka ya fito bainar jama’a yana musayar zafafan kalamai da sa’o’in mahaifinsa.
    Shin me ya sa ake samun irin wannan?

    Don jin amsar wannan tambaya da ma wasu sai ku biyo mu a cikin shirin Daga Laraba na wannan makon.

    続きを読む 一部表示
    30 分
  • Da Gaske Ciwon ’Ya Mace Na ’Ya Mace Ne?
    2024/10/09

    Sau da yawa akan samu rashin fahimtar juna a duk lokacin da wata mu’amala ta haɗa mata.

    Misali, a asibiti wajen haihuwa mata sun sha kokawa da yadda suke ce ’yan uwansu suna nuna musu rashin tausayi.

    Shirin Daga Laraba zai tattauna a kan wannan lamari, ya kuma auna shi a kan mizanin magamar da matan kan yi cewa “Ciwon ’ya mace na ’ya mace ne”.

    続きを読む 一部表示
    30 分
  • Da Gaske ’Yan Arewa Ba Sa Fita Kasashen Waje?
    2024/10/02

    Wata muhawara da ta karade shafukan sada zumunta a kwanakin nan ita ce ko ’yan Arewa, musamman Hausawa, suna fita kasashen waje.

    Duk da wannan ba wani sabon abu ba ne, batun ya dauki sabon salo ne a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da TikTok, inda ’yan kudancin Najeriya suke wallafa fayafayen bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa kasashen waje?

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan batu.

    続きを読む 一部表示
    28 分